Jami’an tsaro sun kashe ‘yan Bindiga 2 tare da kwato makamai a hannunsu a jihar Kaduna.
Lamarin ya farune a yankin Rijana dake karamar hukumar Kachia.
Sojojin sun kuma kai samame a Amale, Gidan Jatau, Gidan Danfulani, da Gidan Duna.
Sojojin sun kwato Bindigar AK47 guda 2 da mashin da wayar hannu da sauransu.