
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa bai kamata ace masu satar kudin talakawa suna kai kudaden kasashen turawa ba.
Dangote yace babu kasar da ba’a sata, amma banbancin misalin kasashen Asia dana Afrika shine, idan sun saci kudin suna zuba jari dasu ne a kasashen su maimakon kaiwa kasashen Turawa.
Dangote yace ba wai yana karfafawa jami’an gwamnati satar kudin talakawa bane amma yana da kyau su san cewa kamata yayi su rika amfani da kudin a cikin gida maimakon kaiwa kasar waje dan ci gaban kasar.