
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa manyan mutane masu fada aji a kasarnan ne suka kirkiri matsalar tsaro a Najeriya.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro inda aka tattauna matsalar tsaro a jihar Filato ranar Laraba inda ya zargi masu fada aji da kawo matsalar tsaro a jiharsa.
Yace wadanda suka kirkiri matsalar zasu iya magance matsalar tsaron idan suka ga dama.
Yace idan irin wadannan manyan mutanen suka hada kai dan jagorancin mutane ta hanyar da bata kamata ba, za’a ci gaba da fuskantar matsalar tsaro duk shekara.
Yace masu fada ajinne ke kara ruruta wutar rikicin ta hanyar zuga mutane akan ci gaba da rikicin.
Ya jawo hankalin cewa, masu fada aji ya kamata suna karfaa zaman lafiya ne tsakanin al’umma.