
Tsohon hadimin shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri yace shine ya taimakawa Peter Obi ya zama mataimakin Atiku a zaben shekarar 2019.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi, saidai magoya bayan Peter Obi sun karyatashi.
Dalilin hakane ya ce zai bayyana shaidunsa.
Ya dakko sakon Email da Peter Obi ya aika masa takardunsa.
Yace Peter Obi yayi ta kiranshi dan ganin ya taimaka masa ya zama mataimakin Atiku inda har ta kai ga ya daina daukar wayarsa.
Yace Atiku yace masa a wancan lokacin ya samo masa mutum me nagarta daga yankun kudu wanda zai zamar masa mataimaki.
Yace kuma akwai mutane 2 da suka fi Peter Obi cancanta amma saboda yana girmama mutumin da ya hadashi da Peter Obi shiyasa ya hada Atiku da Peter Obin.