Monday, December 16
Shadow

Aikin Hajji: Karin Wani Mahajjacin Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi ta sanar da rasuwar wani Mahajjacin jihar a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar yada labarai ta Kebbi Hajj 2024 ta fitar a ranar Lahadi.

Shugaban hukumar Alhaji Faruku Aliyu-Enabo ya bayyana sunan marigayin da Abubakar Abdullahi wanda ya fito daga Gulma a karamar hukumar Argungu.

A cewar Aliyu-Enabo, Abdullahi ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa Gwamna Nasir Idris ya nuna alhininsa kan rasuwar tare da yi wa marigayin addu’a, inda ya roki Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Jannatul Firdaus.

Karanta Wannan  An bayyana ranar da mahajjatan Najeriya zasu fara dawowa gida

“Gwamnan ya kuma bukaci iyalan mamacin da abokan arziki da mahajjatan Kebbi da su jajirce wajen karbar nufin Allah Madaukakin Sarki cikin aminci,” inji Aliyu-Enabo.

Ya ce an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan sallar jana’izarsa a Masallacin Al-Ihram (Ka’aba) a ranar Juma’a.

Wannan lamari dai ya biyo bayan rasuwar wani alhajin jihar Kebbi Tawalkatu Busare Alako daga karamar hukumar Jega, wanda ya rasu a ranar 27 ga watan Mayun 2024 bayan gajeruwar rashin lafiya.

A ranar 28 ga watan Mayu, 2024, wani Mahajjacin jihar Legas mai suna Oloshogbo Idris ya rasu a Makkah jim kadan bayan ya dawo daga dawafin dakin Ka’aba mai alfarma.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka'aba a Najeriya dan koyawa Alhazai yanda zasu yi aikin Hajji, saidai wasu sun ce hakan Bidi'a ne saboda Annabi(SAW) bai ce a yi ba

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *