
Jam’iyyar APC tace akwai karin Gwamnoni 5 da zasu koma jam’iyyar nan da watanni 2.
Mataimakin shugaban jam’iyyar daga yankin kudu maso gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi a jaridar Punchng.
Ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano, da daya daga cikin gwamnonin Abia ko na Enugu ne zasu koma jam’iyyar APC.
Yace wannan ba jita-jita bane, tabbas ne kuma nan da watanni 2 kowa zai tabbatar da hakan.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC inda yace zai je ya kula da lafiyarsa.