Friday, December 5
Shadow

Ji yanda Matasan jihar Anambra ke soyayya harma da aure dan kawai su rika haihuwar jarirai suna sàyàrwà

Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya, NAPTIP tace matasan jihar Anambra sun baci da dabi’ar sayar da jarirai.

Kwamandar hukumar ta jihar, Ibadin Judith-Chukwu ce ta bayyana hakana wata sanarwa data fitar inda tace abin yayi yawa tsakanin matasa.

Tace abin yafi kamari a kauyuka dan hakane suka kafa wata tawaga ta musamman dan yaki da wannan mummunar dabi’a.

Ibadin Judith-Chukwu tace matashi zai yiwa yarinya ciki dai ya aureta amma tana haihuwar jaririn sai ya lalaba ya saceshi ya sayar bada sanin mahaifiyar ba.

Tace amma suna ta kokarin wayarwa da mutane kai game da lamarin.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Dangantaka tsakanin Amurka da Israyla na kara tsami, yanzu haka mataimakin shugaban kasar Amurka, JD. Vance ya soke ziyarar da yake shirin kaiwa kasar saboda rashin jin dadin fadada hàrè-hàrèn da Israyla ke kaiwa Gàzà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *