
Jam’iyyar APC ta yi magana kan rade-radin dake jawo cewa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar.
Hakan na zuwane bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC inda ake ta samun rahotannin cewa, yanzu Kwankwaso zai koma jam’iyyar.
Me magana da yawun jam’iyyar APC a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV yace babu wannan maganar.
Yace bai san komai ba game da rahotannin dake yawo cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC ba.
A wasu rahotannin dai har cewa aka yi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai dauki Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.