Friday, December 5
Shadow

Labarin cewa an cire George Akume wanda kiristane daga mukamin sakataren gwamnatin tarayya, an mayeshi da musulma, Hadiza Bala Usman ka iya jawo rikicin addini>>Inji Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN

Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN reshen Arewacin Najeriya tace labarin karya da aka rika yadawa cewa an cire George Akume daga mukamin sakataren gwamnatin tarayya tare da mayeshi da Hadiza Bala Usman ka iya jawo rikicin addini a kasarnan.

Shuhaban kungiyar, Rev. John Joseph Hayab ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a Kaduna.

Yace Cire George Akume daga mukamin sakataren Gwamnatin barazana ce kai tsaye ga kiristanci, inda yace George Akume na daya daga cikin wakilai kalilan na kiristoci a cikin gwamnatin tarayya.

Yace wanda suka kirkiro labarin da yadashi sun yi ne da wata manufa ta kawo rikici musamman na addini, musamman ganin cewa dama su kiristoci suna sane da cewa ana nuna musu wariya musamman a mulkin gwamnatin musulim musulim.

Karanta Wannan  Bidiyo: Na tafka Kuskure sosai a rayuwata, ko makiyi na ban so ya shiga wahalar dana shiga, Akwai sanda ake ta so a aureni, naki amma yanzu kuma so nake in yi aure kamin in koma ga mahalicci na>>Inji Ummi Nuhu a sabuwar hirarta

Yace dan haka suna kira ga jami’an tsaro dasu binciko wanda suka kirkiro wannan labarin karya da kuma hukuntasu.

Yace suna gayawa George Akume cewa kada wannan ya razanashi suna tare dashi sannan kuma sun yaba da yanda Gwamnatin tarayya ta yi gaggawar fitowa ta musanta labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *