Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Wani manomi a jihar Kebbi me suna Kabiru Kamba ya ce ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta amma bata mutu ba a gona.

An binne jaririyar a gonarsa dake Kamba karamar hukumar Dandi dake jihar.

Ya bayyana hakane ga tawagar hukumar yaki da cin zarafi ta jihar da ta kai masa ziyara gida.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa, tsohuwar babbar sakatariya a jihar, Hajiya Rafa’atu Hammani.ce ta jagoranci tawagar zuwa gidan Kabiru.

Yace a ranar da lamarin ya faru ya je gona sai yaga kunya wadda bai san da ita ba kuma ta yi sama sosai

Yace anan ya kira mutane suka tayashi suna tonawa sai suka ga jaririya.

Karanta Wannan  'Yan shi'a sun gargadi Gwwmnatin tarayya ta sakar musu mutanensu ko kuma su kai kara kotu

Yace sun sanar da ‘yansandan kusa da gurin inda yace kuma ya dauki yarinyar zai rike kuma an yi sa’a ma matarsa ta haihu dan haka ba za’a samu matsalar shayarwa ba.

Yace matarsa ta amince zata rike yarinyar kuma zasu mata suna har ya siyo ragon suna da sauran kayan da ake bukata.

Hajiya Rafa’atu Hammani tace zasu kaiwa matar Gwamna bayanin abinda ya faru sannan sun bashi tallafin kayan kula da yarinyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *