
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne zai yiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah a birnin Madina.
Hakan na zuwane yayin da rahotanni ke cewa, Sarki Aminu Ado Bayero ma yace Santata ya bar masa wasiyyar cewa shine zai masa sallah.
A yanzu dai gawar marigayi Aminu Dantata ta isa Birnin Madina kuma ana jiran mahukunta birnin ne su bayyana lokacin da za’a masa sallah.
A hukumance, ba’a sanar da wanene zaiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah ba.