
A jiya da magariba ne lokacin kasar Saudiyya akawa Marigayi, Aminu Dantata, Sallah aka kuma binne gawarsa a Madina, kamar yanda ya bar wasiyya.
Dangote, da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, dana Jigawa, Umar Namadi, da Ministan tsaro, Abubakar Badaru wanda ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya da sauran manyan mutane ne suka halarci wajan jana’izar.
Dantata, duk da a Madinane yayi jama’a kai kace a Najeriya ne aka yi jana’aizar tasa.
Mina fatan Allah ya kai rahama kabarinsa da sauran al’ummar musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.