
Me sayar da maganin Gargajiya, Al-Hikima ya fito ya janye kalaman sukar da yakewa ‘yan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.
Yace ya janye kalaman ne bayan da Rarara ya kirashi ya bayyana masa cewa hakan bai kamata ba.
Yace A’isha Humaira ma ta kirashi ta bayyana masa rashin kyautawarsa.
Saidai yace ba dan wasu yara wadanda bama ‘yan Kannywood ne yasa ya fito yayi wannan kalami na bad hakuri ba.
A karshe dai ya bayyana cewa, yana da abokai da aminai a Kannywood sosai