
‘Yan kasuwa masu gidajen man fetur sun ki rage farashin man fetur dinsu duk da rage farashin man fetur din da matatar man fetur ta Dangote ta yi wadda da yawansu daga can suke saro man.
Sun bayyana cewa, zasu iya tafka Asara idan suka rage farashin man fetur din nasu.
Sun ce ba zai yiyu su sayar da man fetur din da suke dashi ba a sabon farashin har sai wanda suka saya da tsada ya kare.
A ranar Litinin ne matatar Man fetur ta Dangote ta bakin kakakinta, Anthony Chiejina ta sanar da rage farashin man fetur din daga Naira 880 akan kowace lita zuwa Naira 840 akan kowace lita.
Yace sabon farashin zai fara aiki ne ranar 30 ga watan Yuni.