
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Bode George ya bayyana cewa mulki ba zai koma Arewa ba a shekarar 2027 ba sai shekarar 2031.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga komawar su Atiku jam’iyyar ADC.
Yace duk jam’iyyar da zasu koma su koma amma mulki ba zai koma Arewa ba.
Bode George ya bayyana irin abinda Atiku yake yi da cewa ba na mutane wayayyu bane.
Bode George yace idan mutum gidansa ya lalace ba gyarawa ya kamata yayi ba? Yace fitar su Atiku ta nuna kawai lokacin nasara da jin dadi suke so amma ba zasu iya daurewa lokacin wahala ba.
Yace amma dai ko menene suka yi, masu zabene dai zasu yanke shawarar wanda suke son zaba.