Friday, December 5
Shadow

Masu fita daga PDP zama su dawo ne saboda jam’iyyar mu ce kadai zata iya kada Tinubu>>Inji Shugaban PDP

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta gargaɗi ƴanƴanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam’iyyar, shugaban jam’iyyar na ƙasa Amb. Iliya Damagum ya ce jam’iyyar za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga haɗakar.

Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam’iyyunsu.

“Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam’iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai na san dole za su dawo”, in ji shi.

Karanta Wannan  GANI YA KORI JI: Dai-dai ko gurguwar shawara: Wani mutum ne zai yi sabon gini shine ya tarar da shuri, a madadin ya rusa shi sai ya barshi ya zagaye wajen ya yi gininsa a haka

Shugaban riƙon ya kuma gargaɗi ƴan PDP da ya ce suna ƙoƙarin ”sayar da jam’iyyar”.

Kawo yanzu dai akwai jiga-jigan PDP cikin sabuwar haɗakar ta ADC, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata.

A farkon makon nan ne dai jam’iyyar PDP ta gudanar da taronta na kwamitin zartaswa da a ciki ta ce ta ɗinke ɓarakar da ta ɗauki tsawon lokacin tana fama da shi cikin jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *