
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba zasu yadda a tsayar da dan Arewa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar ADC ba.
Amaechi na daga cikin wadanda suka fice daga jam’iyyar APC suka koma ADC ta hadakar ‘yan Adawa.
Amaechi ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace amma ya yadda kwarewa da cancanta ne zasu samar da shugaban kasa.
Amaechi yace zabe me zuwa za’a buga ne tsakanin ‘yan Najeriya Talakawa da manyan ‘yan siyasa.
Yace ba zai yiyu a yi Dimokradiyya ba a yayin da wani bangare na kasarnan yayi kaka gida a bangaren Mulki ba, dolene suma kudu a basu dama su samar da shugabanci.