‘
Yar gwawarmaya, A’isha Yesufu ta bayyana tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin mutum me halaye masu wuyar sha’ani.

Tace El-Rufai na da Fushi ga kuma riko da ramuwar gayya, sannan yana kokari wajan ganin ya kammala duk abinda yasa a gaba.
Ta bayyana hakane a shafinta na X inda tace amma wannan duka zasu yi amfani wajan gina kasa.
Saidai da yawa sun soketa da cewa, a baya tana daga cikin masu sukar El-Rufai.