
Wani malamin Addinin Islama, Sheikh Saidu Aliyu Maikwano ya bayyana cewa, baya halatta ga musulmi yawa kasar Iran Addu’a ta yi nasara aka kasar Israyla.
Ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyon sa da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Malamin ya kara da cewa, Iran makiyan Musulmai ne na boye, yayin da Israyla kuma makiyan musulmai ne na bayyane dan haka babu wanda nasararsa ko rashin nasararsa zai amfanar da musulunci.
Malamin ya kara da cewa, Sheikh Aminu Daurawa dan Shi’a ne shiyasa yake cewa awa kasar Iran addu’a.
Malamin yace