Saka rigar mama da ta matse ki na iya kawo zafin kan nono, hakanan lokacin jinin Al’ada ma budurwa na iya yin fama da zafin nono.
Tana iya yiyuwa ciwo ne ko kuma infection ya kamaki.
Yawancin mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 40 na fana da ciwon kan nono.
Wata kila tana iya yiyuwa magani ne kika sha ko kuma wani abinci ya miki reaction shiyasa kike jin hakan.
Maganin zafin kan nono ga budurwa:
Saka Rigar mama data yi daidai da nonoki zai taimaka wajan rage zafin.
Zaki iya tanbayar likita ko me kemist ya baki magani.
Rage shan chocolate, shayi, da lemunkan kwalba irinsu Fanta da Coke.
Kina iya samun tsumma me sanyi ko dumi ki rika dorawa akan nonon.
Motsa jiki akai-akai ma na taimakawa.
Ki ragewa kanki damuwa da bacin rai.
Lokacin da ya kamata ki ga likita
Idan wadannan abubuwan suka faru, ki gaggauta ganin likita.
Zafin kan nonon yaki warkewa duk da shan magani.
Yana tafiya ya dawo akai-akai.
Yana fitar da ruwa sosai ko kuma yana kara girma fiye da kima.
Allah ya sauwake.