
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yana kokarin ganin ba ayyukan gina tituna da sauransu kadai bane Gwamnatinsa ke yi, hadda ma kokarin ganin mutanen Najeriya sun bashi amici da yadda.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin kaddamar da titin Aguma Palace–Radio dake Gwagwalada wanda Ministan Abuja, Nyesom Wike yayi.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ne ya wakilci shugaban a waja taron.
Yace wannan titi zai taimakawa ‘yan kasuwa da saran Al’ummar yankin sannan yace wannan alamace ta cewa gwanatinsa na bi sako da lungu dan gudanar da ayyuka ci gaba.