
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, babu maganar ya zama mataimakin Atiku.
Ya bayyana hakane a hirar da Channels TV suka yi dashi.
Yace babu wanda yayi magana dashi akan cewa ya zama mataimakin Atiku.
Yace Takarar shugaban kasa zai nema.
Peter Obi ya kara da cewa, gamayyarsu ta ADC zata samar da dan takarar shugaban kasa nagartacce wanda zai yi Nasara.
Ya kuma ce zamansa a hadakar ‘yan Adawa bata fitar dashi daga jam’iyyar Labour Party ba.