
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya soki Atiku Abubakar inda yace ya cika canja jam’iyyar siyasa.
Wike ya tambayi cewa, shin wai ko a tsilla-tsilla aka haifi Atiku ne.
Wike yace mulki ne kawai ‘yan Adawar ke son samu duk wani abu da suke yi.
Ya kuma caccaki Peter Obi da yace wai Dimokradiyya baymta aiki a Najeriya, Wike yace Peter Obi na fadin hakane sabod bashi ne akan mulki ba.
Yace amma lokacin yana gwamnan jihar Anambra, Dimokradiyya na aiki kenan koh?