
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ya baiwa sojojin Najeriya umarnin Murkushe dukkan masu tayar da kayar bara don kawo rashin hadin kan Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin mataimakinsa, Kashim Shettima a wajan taron ranar sojoji da aka gudanar a Murtala Square dake Kaduna.
Shugaban ya bayyana goyon bayansa ga sojoji da kuma dukkan sauran jami’an tsaro wajan samar da tsaro a kasarnan.
Shugaban yace yana goyon bayan sojojin su murkushe dukkan masu kawowa Najeriya barazana.