
Tauraruwar kafafen sada zumunta Munirat Abdulsalam ta bayyana cewa, Ta zabi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a matsayin masoyi.
Ta bayyana hakane bayan da wani kirista ya aika mata da sakon cewa ta koma kiristanci.
Munirat ta bayyana cewa, babanta masu maganar basu kai shi son Yesu ba amma tun tana da shekaru 13 ta kai kanta masallaci ta musulunta.
Ta bayar da labarin yanda ake kaisu coci suna da shekara 5 a ce su rufe ido a kawo alewa, sai a dauke ace Muhammadu(Sallallahu Alaihi Wasallam) ne ya dauke sai a sake cewa su rufe ido a kuma daukewa ace Yesu ne ya dawo musu da ita.
Tace ita kuma tun a wannan lokacin ta fara jin tana son Annabi(Sallallahu Alaihi wasallam).
Tace idan ba’a daina damunta akan ta koma Kirista ba, zata yi tone-tone ko da kuwa zata rasa ranta bata damu ba.