
An ga Bidiyon matar G-Fresh Al’amin ‘Yar Yola tana wakar cewa, zama da gara Sara ne.
Hakan ya biyo bayan wallafa Bidiyon Sadiya Haruna da GFresh yayi inda aka ganshi yana bata ruwan sha a baki.
Lamarin ya jawo cece-kuce tsakaninsu inda aka ga Gfresh na cewa, zai ci mutuncin wasu mata dake zuga matarsa
Da yawa dai sun ce Gfresh bai kyauta ba inda wasu kuma ke cewa itama matar bata kyauta ba saboda yin cece-kuce da mijinta a Duniya ta ji.