
Hukumar shirya jarabawar JAMB ta saka makin 150 a matsayin mafi karancin maki na shiga jami’a.
Sannan ta saka maki 100 a matsayin maki mafi karanci na shiga kwalejojin kimiyya da fasaha da na Ilimi.
Sannan ta saka makin 140 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun koyar da aikin jinya.
An amince da wannan maki ne a zama da aka yi tsakanin wakilan shuwagabannin jami’o’in da shugaban hukumar JAMB, Prof. Is-haq Oloyede, a Abuja ranar Talata.