Friday, December 5
Shadow

Za’a kori Peter Obi daga jam’iyyar Labour Party saboda ya shiga hadakar ‘yan Adawa ta kayar da Tinubu

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Jam’iyyar Labour party ta sanar da shirinta na korar dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi saboda shiga gamayyar ‘yan adawa dan ganin an kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe a 2027.

Wakilin jam’iyyar, Abayomi Arabambi ne ya bayyana haka a hirar da aka yi dashi a Channels TV ranar Talata inda yace ci gaba da hadaka da Peter Obi ke yi da ‘yan Adawar alhalin yana cewa shi dan Labour Party ne ya sabawa dokar tsarin Mulki kuma ba zasu amince da hakan ba.

Yace zasu yi taro na musamman dan tattauna batun dakatar da Obi daga jam’iyyar su dan bazai yiyu yana nan yana can ba.

Karanta Wannan  Dan jarida ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shikafa zuwa cikin Najeriya

Peter Obi na daga cikin ‘yan siyasar Adawar da suka yi taro suka koma jam’iyyar ADC dan hada kai kamin zaben shekarar 2027 su kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *