
Wani da ake cewa na Annabi ya yiwa Sheikh Lawal Triumph gargadin cewa nan da awanni 24 ya fito ya janye kalaman jingina kwarkwata ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da yayi.
Yace idan bai janye kalaman nasa ba, zasu yi abinda bai kamata ba.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok inda yace su idan aka taba Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) basa kyalewa.
Sheikh Lawal Triumph dai ya karanto Hadisi dake cewa, Ana cire Kwarkwata akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).