
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyanawa hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF cewa ba zai yiyu ya gyara Najeriya a cikin shekaru 2 ba.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin hadiminsa, Tope Fasua a wata hira da aka yi dashi a kafar Channels TV.
Ya bayyana cewa abin takaici ne ace suna kan gyara ba’a gama ba amma ai ta kira ana cewa, wai basa kokari.
Yace a dakata su gama gyaran da suke sannan a musu hukunci.
Yace wadannan kalamai na hukumar IMF zasu iya tunzura ‘yan Najeriya game da gwamnatinsa musamman yanzu da ake fama da matsin tattalin arziki.