Friday, December 5
Shadow

Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta sanar da janye yajin aiki

ASUU ta dakatar da yajin aiki bayan gwamnatin tarayya ta biya albashin watan Yuni.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta janye barazanar shiga yajin aikin da ta yi a baya, bayan biyan albashin watan Yuni 2025 ga membobinta da aka yi jinkiri.

Shugaban reshen ASUU na Jami’ar Abuja, Dr. Sylvanus Ugoh, ya tabbatar da hakan a wata hira da jaridar LEADERSHIP a ranar Talata.

Dr. Ugoh ya ce ƙungiyar ta dakatar da shirin janye ayyuka ne bayan da aka fara ganin albashin watan Yuni a asusun membobin kafin ƙarewar wa’adin ƙarfe 11:59 na dare da reshen ya bayar.

“Albashin watan Yuni na membobinmu ya fara shiga kafin ƙarshen wa’adin ƙarfe 11:59 na daren Litinin, 7 ga Yuli, 2025 da ASUU UniAbuja ta bayar. Don haka, reshen bai fara janye ayyuka ba kamar yadda majalisar ƙungiya ta yanke a baya,” in ji Ugoh.

Karanta Wannan  Kalli Hoton Sojan da me kwacen waya ya Kàshè a Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *