
Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da kai hari gidan Sarkin Kano na 16 la, Malam Muhammadu Sanusi ll a Kofar Kudu a ranar Lahadi.
Freedom Radio ta rawaito cewa, Mai magana da yawun rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi ya tabbatarwa jaridar PUNCH hakan ta cikin wani sakon WhatsApp da ya aike musu a yau Talata.
A cewar Kiyawa sun kama mutane hudu kuma suna ci gaba da gudanar da bincike a kansu.