
Rahotanni na cewa an matsawa Atiku Abubakar ya hakura ya hakura da takara a shekarar 2027 ya barwa dan kudu.
Rahoton yace Atiku ya janyewa dan takara daga kudancin kasarna bayan wani zama da aka yi dashi.
Saidai a martaninsa, Atiku yace wannan rahoton karyane, bashi da tushe ballantana makama.
Atiku yace wannan kawai shiri ne na su Tinubu dan ya raba kawunan ‘yan Adawa.
Atiku ya kara da cewa, babu abinda zai raba kansu, sun mayar da hankali wajan ganin sun cimma burinsu na kayar da shugaban kasar zabe.