
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya bayyana cewa, shi daka can ko da yana APC Munafurtar jam’iyyar yake.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi wadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Babachir yace APC da Wike sune suka koya musu munafurci a siyasa, kana cikin jam’iyya amma kanawa wata jam’iyyar aiki.
Ya bayyana cewa suna son su canja Gwamnatin Tinubu ne saboda ya ci amanarsu.