
Hukumar shirya jarabawar Jami’a ta JAMB ta sanar da jihohin Anambra da Imo a matsayin wadanda aka fi yin satar amsa.
A bayanan da hukumar ta fitar ranar Talata ta fitar da cibiyoyin da aka kama ana satar amsa a cikinsu.
Gaba daya an kama Cibiyoyi 19 ne a fadin Najeriya.
A jihar Anambra ne aka fi kama masu yawa inda ake da guda 6, Sai guda 4 da aka kama a jihar Imo, An kama guda daya a Abia, hakanan an kama guda daya a Edo.
A jihar Kano guda 2 aka kama.
sai guda 1 da aka kama a kowane jihohin, Ebonyi, Delta, Kaduna, Rivers da Enugu.
Shugaban hukumar JAMB din, Prof. Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan.