
Gwamna Kano, Abba Kabir Yusuf na shan yabo bayan da aka ga ya sa an karawa wani me daukar hoto girma.
Rahoton yace Gwamna Abba ya san me daukar hoton tun shekarar 1999, sai kuma a yanzu ya sake ganinsa.
Ya tambayi me daukar hoton a wane matsayi yake? Inda ya gaya mai, nan take ya bayar da umarni ga kwamishinan yada labarai cewa a baiwa me daukar hoton mukami.
Wannan abu yasa mutane da yawa sun jinjinawa Gwamnan.