
Rahotanni na cewa rashin Amincewar Najeriya ta karbi ‘yan kasar Venezuela masu laifi daga kasar Amurka baiwa shugaban kasar Amurka, Donald Trump dadi ba.
Rahoton yace kasashe kusan 5 ne na Afrika Amurka ta nemi su karbi masu laifin hadda Najeriya amma Najeriya taki amincewa.
Dalili kenan da shugaban Amurkar Donald Trump ya ji haushi ya kakabawa Najeriya takunkumi kan shiga Amurka.
Rahoton yace wannan takunkumi zai ci gaba da zama akan Najeriya har sai Najeriyar ta amince da bukatar kasar Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na amfani da irin wannan dabarar ta kakabawa kasashe takunkumi har sai sun masa abinda yake so.