
A wani littafi da ya wallafa, wanda aka ƙaddamar a ranar Talata, mai taken ‘According to the President: Lessons from a Presidential Spokesperson’s Experience’, Garba Shehu, kakakin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce labarin shigar ɓeraye cikin fadar shugabanm ƙasa, Vila, ba gaskiya ba ne.
A cewar Garba Shehu, an ƙiƙiri labarin ne don kauda hankalin ƴan ƙasa daga rashin lafiyar Buhari a wancan lokaci.