Friday, December 5
Shadow

Karka Dauka Adawace: Da gaske ana wahala a Najeriya>>Atiku ya gayawa Tinubu

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa da gaske ana wahala a Najeriya.

Atiku yace rashin tunani da zumudi yasa gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur wanda tun daga wancan lokaci gwamnatin ta jefa ‘yan Najeriya ramun talauci da fatara Wanda har yanzu basu fito ba.

Atiku yace a kokarin kawar da wahalar da gwamnatin ce ta jawo ta da kanta, Gwamnatin Tinubu ta yi kokarin biyan ma’aikata tagomashi kamin karin albashi na Naira dubu 35 duk wata.

Atiku yace amma kamar sauran Alkawuran gwamnatin sai abin ya sha ruwa, Atiku yace Ma’aikatan na bin Gwamnati bashin kudin tagomashin data musu Alkawari na watanni 10 amma na watanni 6 kawai aka biya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Aka baiwa Hammata Iska tsakanin Magoya bayan Chelsea da na Barcelona a gidan Kallon bayan wasan daren jiya

Dan haka Atiku yayi kira ga gwamnati data biya na sauran watanni 4 da ake binta wanda kowane ma’ikaci zata biyashi Naira 140,000 kenan.

Atiku yace gwamnatocin jihohi sun yi kokari wajan biyan ma’aikata da kyautata musu amma a bangaren gwamnatin tarayya sai ta gaza.

Atiki ya kara da cewa, abin takaici shine yanda gwamnatin ta kama wani ma’aikaci me suna Comrade Andrew Uche Emelieze sa yayi yunkurin shirya zanga-zanga dan neman a biyasu hakkokinsu.

Atiku yace wannan zalinci ne dan haka suna neman a saki Comrade Andrew Uche Emelieze da gaggawa ba tare da wani sharadi ba.

Atiku yace Wahalar da ake ciki a Najeriya da gaskene kuma ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ta magance ta.

Karanta Wannan  Rashin tsaro da kashe-kashe sun ragu da kashi 90% a Najeriya, in ji NSA, Ribadu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *