
A wani Bidiyo da aka ga Tauraruwar Tiktok, Sadiya Haruna ta na waya da sabon angonta da aka daura musu aure yayin da ake mata kwalliya, wasu na cewa kamar muryar Garba.
An ji tana magana dashi tana cewa, an daura? Yana ce mata Eh an daura.
Saidai a yayin wasu suka ce Gfresh ne amma wasu aun ce bashi bane duk da muryar ta yi kama da tashi.
Gfresh dai ya bayyana cewa, shine ya sake auren Sadiya Haruna amma ita ta fito tace bashi bane.
Koma dai menene, lokaci be bar komai ba.