
Gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta iso Najeriya.
Rahotanni sun ce yanzu haka za’a tafi da gawar zuwa Daura dan mata sutura.
Tun a jiya ne dai Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya bayyana cewa a yaune za’a wa gawar tsohon shugaban kasar Sutura.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne suka je kasar Ingila suka taho da gawar.