
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun sake komawa Kabarin Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari suka asa Addu’a da safiyar yau Laraba.
Tun a ranar Litinin El-Rufai ya je garin Daura a yayin da shi kuma Atiku yana garin Daura tun ranar Talata.
A jiyan Jama’ar Daura sun yiwa Atiku kyakkyawar tarba.