
Diyar Tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, Noor ta wallafa wani sako a shafinta na sada zumunta kan rasuwar mahaifinta da ya dauki hankula.
Hakan na zuwane kwana daya da rufe mahaifinta a kabarinsa.
Noor ta wallafa cewa “Tace tana cikin jimamin rashin ganin irin rayuwar data shirya musu ita da mahaifinta. Tace zata ci gaba da tunawa dashi a ko da yaushe. Tace tana Addu’ar Allah ya baiwa magaifinta Aljannah.
Noor na daga cikin ‘ya’yan Buhari mata da ya bari.