
Rahotanni sun bayyana cewa, Rashin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari yasa jam’iyyar APC na fuskantar ficewar ‘yan jam’iyyar CPC daga cikinta.
Rahoton yace tuni ‘yan CPC suka fara ficewa daga APC zuwa sabuwar jam’iyyar hadaka ta ADC.
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewa, ‘yan CPC dayawa dake cikin APC sun koma jam’iyyar ta ADC.
Hakan na zuwane bayan da tsohon shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar yace mutuwar Buhari zata canja fasalin siyasar Najeriya.