
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, a yau, Juma’a ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai je jihar Kano da yiwa oalan Aminu Dantata da sauran Al’ummar jihar gaisuwa.
A ranar 28 ga watan Yuni ne dai Aminu Dantata ya rigamu gidan gaskiya inda aka binneshi a Madina kusa da kabarin matarsa
A lokacin da Dantata ya rasu, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu baya Najeriya amma ya aika wakilai da suka halarci ta’aziyyar Dantata.