
Rahotanni sun bayyana cewa har an canja sunan jami’ar UNIMAID dake Maiduguri zuwa sunan Muhammadu Buhari University.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
A jiya ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin canja sunan jami’ar zuwa sunan tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.