
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta bayyana cewa, suna binciken gwamnoni masu ci dake kan kujerunsu a halin yanzu haka guda 18.
Shugaban EFCC din, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a Legas ranar Juma’a data gabata.
Yace a yanzu suna kan binciken gwamnonin ne amma idan suka sauka daga mukaman su na gwamnoni za’a shiga mataki na gaba a binciken.