
Kada Ki Kuskura Ki Sake Shigowa Majalisa, Gargaɗin ‘Yan Majalisar Dattaawa Ga Sanata Natasha
Daga Muhammad Kwairi Waziri
A wata sabuwar sabani da ke kara dagula lamura a Majalisar Dattawa, wani sashe na majalisar ya fitar da gargadi mai zafi ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda suka ce:
“Kar ki kuskura mu ga ƙafarki a majalisar dattijai domin har yanzu ki na ƙarƙashin dakatarwarmu.”
Wannan gargadi na zuwa ne kwanaki bayan Sanata Natasha ta sanar da shirinta na komawa kujerarta a majalisar ranar Talata mai zuwa. Majalisar ta nuna cewa akwai hukuncin dakatarwa da har yanzu ba a janye ba, kuma duk wani yunkuri nata na komawa za a ɗauka a matsayin sabawa doka da ka’ida.
Sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken bayani daga ofishin shugaban majalisar kan ainihin dalilin dakatarwar ko matakin da za a ɗauka idan ta bayyana a zauren majalisa ba.
A halin yanzu, ana sa ran wannan sabanin zai janyo cece-kuce a tsakanin magoya bayanta da masu riko da tsarin majalisa, musamman ganin cewa Natasha na daya daga cikin sanata mata da suka fito da karfi a zaɓen 2023.