Friday, December 5
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda Ya Yi Haɗãri, Ya Samu Rãuɲi A Ƙafa, ji Halin da yake ciki a yanzu

DAGA Muhammad Kwairi Waziri

Rahotanni da suka iso mana yanzu-yanzu na tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya yi mummunan haɗãriɲ mota a hanyarsa ta dawowa daga garin Daura, jihar Katsina.

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa haɗãriɲ ya faru ne sa’o’i kaɗan da suka wuce, kuma ya haifar da fãŝhēwar ƙafar gwamnan, wanda yanzu haka yake karɓar kulawa a Asibitin FMC Daura.

Bayan jin labarin hadarin, jama’a da dama sun fara aika saƙonnin ta’aziyya da addu’o’i na fatan samun lafiya cikin gaggawa, musamman ganin irin nauyin da ke kan gwamnan a wannan lokaci mai cike da kalubale.

Hukumomin da abin ya shafa, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba su fitar da cikakken bayani ba kan yadda hadarin ya faru da kuma halin da gwamnan ke ciki kwata-kwata.

Karanta Wannan  China za ta haramta tsawwala sadakin aure da bikin 'almubazzaranci'

Muna fatan Allah ya ba shi lafiya, ya kuma kare sauran shugabanni da al’umma gaba ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *