
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Musa Asadussunnah ya bayyana cewa ya kamata a karantar da mutane cewa, ba wai su kadai ne ke da hakki akan shuwagabanni ba.
Yace suma shuwagabannin na da hakki akan mutane da zasu nemi Allah ya saka musu.
Yace ko da mutum zaluntarka yayi ka mai Addu’ar da ta zarce ta zaluncin da ya maka to ka yi cuta.
A baya dai malam yace idan aka cuci mutum Allah zai iya yafewa koda me hakkin bai yafe ba.